Bitcoin Hausa

Kids Programs

A zamanin yau, Bitcoin da kuɗin zamani (cryptocurrency) suna ƙara samun karɓuwa a duniya. Yara ma suna da muhimmanci a cikin wannan tafiya, domin su ne gobe.

Muhimmancin Shirin

Shirin nan wata dama ce ga iyaye su fara koya wa ‘ya’yansu ilmin Bitcoin a Hausa tun suna ƙanana. Tunda Bitcoin da fasahar blockchain suna daga cikin manyan abubuwan da ke sauya tattalin arzikin duniya, yara da suka fara fahimta tun da wuri za su samu gagarumin amfani a gaba.

Abubuwan Da Aji Zai Ƙunsa

  • Gabatarwa ga Bitcoin

    Yara za su fahimci menene Bitcoin da yadda yake aiki.

  • Tarihin Kuɗi

    daga kuɗin gargajiya zuwa kuɗin zamani (digital money).

  • Amfanin Bitcoin a rayuwa

    dalilin da yasa ake amfani da shi, da yadda yake sauƙaƙa harkokin kudi.

  • Bitcoin cikin Nishadi

    darussa za su kasance cikin games, misalai, da tattaunawa domin yara su koyi ilmi cikin sauƙi da nishaɗi.

Amfanin Shiga Aji na Bitcoin ga Yara

  • Yara za su samu ilmin kuɗi na zamani (financial literacy) tun suna ƙanana.

  • Za su fahimci tsaro a yanar gizo (cyber safety).

  • Za su fara sha’awar fasaha da coding ta hanyar fahimtar yadda Bitcoin yake aiki

  • Za su samu horon tunanin kasuwanci da fasaha domin tunkarar gobe.